Home Sports Yadda za’a tayar da ginshikan nasarorin da suka ruguje a Kano

Yadda za’a tayar da ginshikan nasarorin da suka ruguje a Kano

by Editor
0 comment
Pillars Fc

Daga: Abdullahi Shehu

Fassarawa: Jamilu Uba Adamu

Gasar ajin kwararrun ta kasa Najeriya NPFL ta 2021/2022 ta kare tare da barin abubuwan tunawa duka marasa kyau da masu kyau. Har yanzu a bin dake ciki tunanin masu sha’awar kwallon kafa a fadin duniya shine faduwa da zakarun NPFL Kano Pillars wanda suka lashe gasar har sau hudu daga gasar Premier bayan shekaru 21. Muhawarar ta fara ne tsakanin magoya bayan masu sha’awar wasanni sama da miliyan 15 kan hanyar da za su bi don tayar da wannan rugujewar Pillar a jiha ta biyu mafi yawan al’umma a Najeriya.

Babu mahawara mai yawa kan dalilin daya daga cikin kungiyoyin da ke samun kudade a kasar ba su iya kammala kakar wasa sama da red zone a NPFL. Daga cikin wasu matsalolin, ana kallon rashin kyakkyawan shugabanci a matsayin babban dalilin da Pillars suka samu kansu a inda suke a yau.

Masu sha’awar kwallon kafa a Kano sun yi kira da a yi wa daukacin shugabannin kungiyar garambawul, domin a maye gurbinsu da wasu matasan masu kuzari. A ganinsu dole ne a baiwa matasa damar tafiyar da al’amuran kungiyar domin abin da suke ganin zai sake karawa Pillars girma. Su wane ne matasan Kano da za su iya rike Pillars?

Na shafe sama da shekaru ashirin ina bibiyar harkar kwallon kafa a Najeriya wanda ya bani damar samun dan karamin ilimi kan yadda kalubalen tafiyar da harkokin kungiyoyin kwallon kafa a Najeriya ke da shi. Idan ka dauki misalin Kaduna Utd da Ranch Bees FC da suke jihar Kaduna,nazari kenan akan makwabciyar jihar ga Kano wanda akwai lokacin da suke da kungiyoyi guda biyu dake fafatawa a gasar NPFL. Duk da irin hazaka da ake da ita a jihar ba ta da wata kungiya a gasar firimiyar kwallon kafa ko daya a halin da ake ciki yanxu wanda kuma matasan da suka yi ikirarin cewa za su iya tafiyar da harkokin kungiyoyin ne a ka wayi gari sun gaza yin kwatan kwacin abinda magabatan su sukayi kuma su ne ke da alhakin halin da wasan yake ciki a jihar.

Komawa jihar Kano da irin nata matasa masu kishin kasa a shirye su sadaukar da komai nasu domin ci gaban wasan.Kasance war ladabi da biyayya sune manyan sinadarai don cimma burin da ake so ya yi karanci a tsakanin wadannan matasa.

A jihar da take da mutane da suka kware wajen shugabancin kwallon kafa a jiha da kasa irin Kano da Nigeria kamar su mai girma Alhaji Ibrahim Galadima da Alhaji Tukur Babangida da Alhaji Abba Yola da Alhaji Abba Galadima da Alhaji Sharif Inuwa Ahlan. Duk sun kai kololuwar gudanar da harkokin kwallon kafa a kasar. Ina shakkun idan matasa da masu kula da kwallon kafa masu zuwa sun yi amfani da tarin ilimin wadannan kwai.

A gefe guda, za mu iya tunawa a sarari cewa irin wannan kira na samar da sabbin matasa da ƙwaƙƙwaran shugabanci ya sa aka naɗa Alhaji Suraj Jambul kuma mun ga sakamakon.

A nawa ra’ayi, idan matasan na son su anshi ragamar gudanar da kungiyar Kano Pillars,Wannan ci gaban maraba ne kuma abin alfahari ne amma ya kamata su sani cewa ba za ka iya zama matukin jirgin sama ba a dare daya ba. Buri da tunanin kasancewar abu sun bambanta da abubuwan da suke a zahiri.Zaifi kyau su kasance masu ladabi ga magabata da kuma hakuri don su koya ya ake gudanar da kungiyar kwallon kafa.

A karshe, na tuna da halin da Kano Pillars ta taba samun kanta makamancin wannan a shekarar 1999.Fadawa wancan ibtila’i ya zama kungiyar da ta dawo da karfi daga karshe ta lashe gasar sau hudu, Federations Cup sau daya, ta kai matakin Semi Final na CAF champions league a karon farko da suka wakilci kasa Nigeria.Duk wannan an cimma shi ne tare da sabunta kudirin yin nasara yayin da aka mika ragamar ga wasu kwararrun a harkar gudanar wa a kwallon kafa ta Najeriya da gwamnati ba za ta amince da wata magana ta biyu kasa da faduwa ba. Wannan aikin bai yi kama da tashin hankalin da ake yi a yanzu ba don jimlar sake fasalin kungiyar.

 Bayani: An rubuta Wannan ainahin labarin da turanci ne a Jaridar wasanni ta Mabiya

You may also like

Leave a Comment