Home Sports Neman Ilimi Tareda Wasanni

Neman Ilimi Tareda Wasanni

- Professor Muhammad Rabiu Chunho

by Editor
0 comment

Masoya da mutanen dake bibiyar wasan Kwallon Kafa, a arewacin Najeriya, musamman Jihar Kano a basu cika tsammanin a akwai alaka tsakanin ilimi da wasan Kwallon Kafa ba.

Kasancewar a lokuta da yawa matasan dake buga wasan Kwallon Kafa Basu cika samun nasara a makaranta ba ko samun damar yin karatu Mai zurfi ba.

Amma sai dai kamar yadda bincike ya nuna, yan Kwallo da yawa a fadin Duniya harma da Nan gida Najeria sun samu daukaka Mai yawa a bangarorin ilimi.

A misalin irin wa Yan Nan Yan Kwallo akwai irin; Socrates na Brazil, Wanda yazama Dockta, Anan gida Nijeria akwai irin su Sir, Segun Odegbami.

Anan gida Jihar Kano kuwa Allah yai Mana baiwar samun wannan bawan Allah da zan kawo sharhi da takaitaccen tarihin sa, musamman akan wasan Kwallon Kafa.

Dan saboda yazama madubi abun dubawa ga na baya, musamman wajen hada wasannin motsa jiki da Neman ilimin addini da na boko.

Ya fara buga Kwallo ne a karamin Kulub dake Mai suna Silver Stone dake unguwar Kofar mazugal, Kuma a yayi wasanni ne na makaranta a lokacin yana karatu a makarantar sakandiren horas da malamai ta Garin Bichi, inda daga nan ne Kungiyar Kwallon Kafa ta super star dake unguwar,makwalla dake cikin birni ke dauko shi a matsayin sojan haya dan ya buga musu Wasa.

A irin wannan wasannin ne ya taimakawa Kungiyar Kwallon kafar ta Super Star samun nasara lashe gasar kofin Dan wawu wacce itace mai daraja ta daya a jihar Kano a wannan zamanin.

Wanda ganin irin bajintar da kwarewar da ya nuna a wannan wasan ne yasa Kungiyar Kwallon Kafa ta Raccah Rovers ta dauke shi dan ya buga Mata Wasa a shekarar 1981, Kuma tai Masa register.

A wancen zamanin shida Abubakar Zagallo (yanzu shine na’ibin limamin masallancin Juma’a a wata Unguwa a New York, America) sune suke buga namba Biyar da shida a Bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Raccah Rovers.

Tsohon Dan wasan Kwallon kafar, ya canza sheka daga Raccah Rovers zuwa Kungiyar Kwallon Kafa ta Bank of the North, bisa kin Yarda da yai da cigaba da bugawa Raccah Rovers Wasa bayan Kungiyar ta chanza suna zuwa Nigerian Breweries, Wanda Kamar yadda ya bayyana mun cewar hakan yanada nasaba da addinin sa na muslunci. Kuma tare da Margayi Usman Dan Lami Akawu Kofar Wanbai, Wanda shima shaharren Dan wasan Kwallon Kafa ne (Allah ya gafarta Masa, Ameen) suka koma wannan Kungiya ta Bank of the North

Ya ajiye takalman sa na wasan Kwallon Kafa ne a shekarar 1989, sai dai Kuma yayin da yake karatunsa na master’s a jami’ar Bayero, an zabe shi a jerin Wanda zasu wakilci kasa Najeriya a gasar Jami’oi ta Duniya a wasan Kwallon Kafa a shekarar 1995.

A zamanin da Professor yake taka wasan na, saboda kwarewarsa a wasan ya samu sunayen inkiya daban-daban Wanda Yan kallo suka lakaba masa; Na Makwalla, Chanhu, Mai Gida a Sama.

Yanzu dai Haka, Mallam Muhammad Rabiu “Chunho” Professor ne a Wanda keda kwarewa an adapted physical education, bangaren kinetics, and health education dake jami’ar Bayero, Kano.

Jamilu Uba Adamu, Mai bibiyar Tarihin wasanni Kwallon Kafa ne.

You may also like

Leave a Comment