Home Sports Akwai gazawar sahukunta a abin takaicin da ya faru a wasan Kano Pillars da takwarta ta Katsina United

Akwai gazawar sahukunta a abin takaicin da ya faru a wasan Kano Pillars da takwarta ta Katsina United

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Daga Jamilu Uba Adamu

Hamayya da adawa tsakanin Magoya Bayan Kungiyoyin Kwallon kafar Kano Pillars da Katsina United tsohon lamari ne Wanda ya dade a tsakaninsu.

Dan haka nema kusan duk lokutan da Kungiyoyin biyu zasu Kara akan ta nadi jami’an tsaro na mysamman Domin Kare afkuwar hatsaniya a tsakanin bangarorin biyu.

A wasu lokuta ma akan bada umarnin yin Wasa a tsakanin su batare da Yan kallo ko Magoya Baya ba.

Hatsaniya da rikici marasa dadi ya sun sha faruwa a tsakanin Kungiyoyin Kwallon kafar dake makwabtan jihohin biyu.

Amma saidai hatsaniyar da aka samu awasan da aka gudanar a jiya Asabar a filin Wasa na Sani Abacha dake unguwar Kofar Mata, a jihar kano, tsakanin Kungiyoyin biyu. Abun ya Yi muni Kwarai da gaske.

Dalilin hakan kuwa, shine wannann Wasa ya kasance na farko a cikin shekara biyu da ita Kungiyar Kwallon kafar ta Kano Pillars ta samu damar dawowa gida jihar Kano Dan gudanar da wasanta. Wanda a Baya take gudanar da shi a Garin Kaduna. Saidai bayan wasu dalilai ta komar da gudanar da wasan nata a filin wasa na Umar Dikko a Jihar Katsina.

A garin na katsina, sun gudanar da Wasa biyu, kwatsam ba zato ba tsammani sai ga takarda ta futo daga hannun hukumar gudanar da wasan Kwallon Kafa na ajin kwarraru ta Kasa (LMC) an umarci Kungiyar data karbi bakwancin Kungiyar Kwallon kafar ta Katsina United a Gidan ta, filin Wasa na Sani Abacha, Jihar Kano.

 Magoya bayan Kano Pillars sun gaza jure fushi.

 Mahukuntan Kungiyar Kwallon kafar ta Kano Pillars tare da Kungiyar Magoya Bayan ta basuyi amfani da wannan damar da suka samu ba, na dawo da Kungiyar gida jihar Kano ba.

Kasancewar ba wani tanadi da akai dan Hana faruwar barkewar rikici da hatsaniya a filin wasan. A mintuna na saba’in da Tara ne alkalin Wasa da Yan Kwallo suka futa daga filin Wasa Dan cetar rayuwar su, bayan afkuwa cikin fili da wasu masu ikirarin Goyan bayan Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars sukai, sun shigo filin da makamai, wasu Kuma na jifa da duwatsu.

A wannnan lokacin wasan Yana kunnen Doki (0-0)

A karshe gurbattun Magoya Bayan Kungiyar Kwallon kafar ta Kano Pillars sun huche haushin su a kan motar Yan wasan ta Katsina United. Inda sukayi wa motar raga-raga.

Yan wasan na katsina United basu samu damar futa daga dakin da aka boye suba a filin wasan, kasancewar wasu gurbatattun Magoya Baya najiran futowar su Dan su ci musu mutunchi, har sai misalin karfe Takwas na dare Kamar yadda na samu labari.

Yan wasan, sunyi asarar wayoyin su, takalma, da wasu abubuwa Masu amfani da suka ajiye acikin motar daukar tasu.

Abun da mafi yawan Masu bibiyar wasan Kwallon Kafa suke Tambaya shine; Wannen shiri mahukuntan Kungiyar Kwallon kafar ta Kano Pillars sukai Dan wajen Kare afkuwar wannan hatsaniyar?

Wane Dalili ne ya janyo mahukuntan LMC suka bada izinin yin wannann Wasa a Kano (Kuma harda Yan Kallo ) duk kuwa da cewar sunfi kowa sannin rikicin da akai tsakanin Magoya Bayan Kungiyoyin biyu a Jihar Katsina, wacce tai Muni Kwarai a Baya?

Bayan sannin da sukai sarai na adawar da Tarihin adawar dake tsakanin Kungiyoyin biyu?

Akwai wata riba ko alfanu da wasu ko wani zai anfana bisa faruwar wannann hatsaniyar?

Wacce rawa ko mataki mahukuntan Kungiyar Magoya Baya suka dauka wajen ganin anyi wasan Lafiya ankuma tashi lafiya, kasancewar sunfi kowa sanin Magoya Bayan Kungiyar?

Wanda suka aiwatar da wannnan aika aika Yan Kungiyar Magoya Baya ne ko wasu ne daban suka aiwatar? Idan wasu ne ba Yan Kungiyar ba, me yasa aka bar su suka batawa Kungiyar Suna?

Meyasa Mahukuntan Kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars basu Samar da kyakkyawan tsaro ba?

Kullum haka za a cigaba ba za ai Gyara da wayar wa Magoya Baya Kai ba musamman aka harkar Goyan Baya batare da rigima da hatsaniya ba?

A Ina Kungiyar zata cigaba da Wasanni nata?

Wannan sune kadan daga cikin tambayoyin dake bukatar Amsa.

Musamman daga wajen mahukuntan Kungiyar Kwallon kafar ta Kano Pillars da Kuma Kungiyar Magoya Baya.

Gaskiyar magana dai koma suwaye suka aiwatar da wannan aika-aika basuyiwa Magoya Baya na Gaskiya da Ita kanta Kungiyar Adalci ba.

Kuma wannan ba nuna kauna ga Kungiyar ta Kano Pillars bane. Illama dai cutar da Kungiyar da Magoya Baya na hakika ne.

A karshe, adduar ta ga Kungiyar, Allah ya dawo da martabarta da daukakar Kungiyar. Allah ya Kuma Kare faruwar irin wannnan lamarin Mara Dadi a gaba. Ameen.

Adamu Mai sharhi da bibiyar Wasan Kwallon Kafa ne jamiluubadamu@yahoo.com

You may also like

Leave a Comment

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00