Home News Karota zata ci gaba da kama babur mara Lamba ɓaro-ɓaro a saman Tanki

Karota zata ci gaba da kama babur mara Lamba ɓaro-ɓaro a saman Tanki

by Isiyaku Ahmed

Daga Nabilusi Abubakar

Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta ce, za ta ci gaba da kama duk Adaidaita Sahun da ba’a rubuta Koriyar Lamba ɓaro-ɓaro a saman Tankin sa ba.

Hukumar ta bayyana haka ne a Litinin din nan, bayan data lura da cewa, duk Baburan Adaidaita Sahun da ake aikata manyan laifuka ba sa rubuta Lambarsu ɓaro-ɓaro a jikin tankin su.

Hukumar dai ta bayyana cewa hakan ya zama wajibi ta ɗauki matakin tilastawa direbobin rubuta lambar don sauƙaƙawa al’umma masu hawa Ɗan Sahun.

Bayanin haka na ƙunshe ne a cikin wata takarda da Kakakin Hukumar ta KAROTA Nabilusi Abubakar Ƙofar Na’isa ya sanya hannu aka rabawa manema Labarai

Ya kara da cewa wasu daga cikin al’umma masu kishin jihar nan ne suka an-karar da Hukumar da nufin ɗaukar matakin da ya kamata domin a shawo kan matsalar.

Nabilisi ya kuma shaida cewa ƙofar Hukumar a ɓude take ga duk waɗanda suke da wani ƙorafi ga matuƙa Baburan adaidaita sahun, da su gabatar da shi ga Hukumar domin ɗaukar matakin daya dace.

A ƙarshe ya yi kira ga ɗaukacin al’umma masu hawa baburan Adaidaita Sahun da su tabbatar sun kwafi ko hadda ce Koriyar Lambar da ke jikin baburan domin sauƙaƙewa Hukumar yin bincike idan buƙatar hakan ta

taso.

Leave a Comment

* By using this form you agree with the storage and handling of your data by this website.