Home Sports Kamalu ya lashe matsayi na farko a gasar sandan Golf na Ola Sa’ad

Kamalu ya lashe matsayi na farko a gasar sandan Golf na Ola Sa’ad

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Daga Jamilu Uba Adamu

A ranar lahadi ne aka kammala gasar cin Kofi ta wasan sanda Golf, wace aka dau kwana hudu anayi a filin wasan sanda na Golf na Ola Sa’ad Ibrahim a barikin Soja ta Jaji-Najeriya.

Dan asalin Jihar Kano Kuma Kwararren Dan wasan Golf Kamalu Bako ya kafa Tarihin lashe matsayi na farko a wannan gasa.

Mallam Kamalu Bako ya kafa Tarihin ne bayan ya samu maki Dari Biyu da tamanin da Tara (289) a rukunin kwararru na gasar.

Kamal Bako shine mataimakin Kwararren Dan wasan sandar Golf na Kano Golf Club dake Bompai.

You may also like

Leave a Comment