Home Sports Zakunan Teranga na kasar Senegal sun lashe Kofin gasar cin Kofin kasashen nahiyar Afrika

Zakunan Teranga na kasar Senegal sun lashe Kofin gasar cin Kofin kasashen nahiyar Afrika

by Isiyaku Ahmed
0 comment

Daga Jamilu Uba Adamu

Kasar Senegal ta samu nasarar lashe Kofin gasar cin Kofin kasashen nahiyar Afrika a Karo na farko, bayan samun nasarar lallasa kasar Masar da ci hudu da biyu a bugun daga Kai sai Mai tsaron gida.

Bayan shafe mintuna Dari da Ashirin ba tareda samun saka kwallo ba a tsakanin kasashen Biyu.

An fafata  wasan karshen na gasar a filin wasa na Paul Biya, Olembe, kasar Kamaru.

Tarihi ya bayana Kasar Senegal tayi rashin Nasara har sau Biyu a irin wannan wasan karshen  a shekarun 2002 da 2019. Inda sukai rashin ga kasar Kamaru da Aljeriya a wasannin karshen.

Dan haka wannna shine Karo na farko da kasar ta fara samun nasarar lashe wannan gasa.

Wannan nasarar tasu itace ta dakatar da kasar ta Masar samun rashin nasarar lashe Kofin gasar har sau takwas.

Kamar yadda Tarihi ya nuna yanzu kasar senegal bisa samun wannan nasara ta shiga jerin rukunin kasashe irinsu;Congo Brazzaville, Ethiopia, Morocco, South Africa, Sudan, Tunisia, Zambia masu nasarar lashe Kofin gasar sau daya.

Sai dai har yanzu fafatawa bata Kare ba a tsakanin wannan kasashe guda Biyu, kasancewar a ranar Ashirin da uku ga watan maris na wannan shekarar ta 2022 zasu sake barje gumi a wasan share fagge na samun damar wakiltar nahiyar Afrika a gasar kwallo na duniya, Mai taken Qatar 2023.

Duk kasar da ta samu rinjaye a wannan wasa itace zata wakilce yankin na Afrika.

You may also like

Leave a Comment